A yau, Alhamis, matasan Kenya suka ci gaba da zanga-zangar da suka fara ta ƙin jinin gwamnati, wadda ta faro sanadiyyar ƙin yarda da ƙarin haraji, wadda ta rikiɗe zuwa buƙatar shugaban ƙasar William Ruto ya yi murabus daga muƙaminsa.
Masu shirya zanga-zangar sun yi barazanar yin tattaki har zuwa fadar shugaban ƙasar da nufin “tsige Shugaba William Ruto,” a cewar wani rahoto da gidan talabijin na Citizen TV mai zaman kansa ya fitar.
Ɗaya daga cikin manyan masu jagorantar zanga-zangar, Kasmuel McOure, ya bayyana zanga-zangar ta yau a matsayin “mafi girman zanga-zanga a cikin duk zanga-zangar da aka yi a ‘yan kwanakin nan,” a wata hira da Citizen TV.
Matasan sun shafe wata uku suna gudanar da zanga-zangar da tuni ta tilasta wa gwamnati janye ƙudirin ƙarin harajin da kuma rusa majalisar ministocin ƙasar.
Jaridar Capital News ta ba da rahoton gagarumin gangami a shafukan sada zumunta, tare da yin kiraye-kiraye a mamaye cibiyoyin gwamnati don nuna adawa da “mummunan shugabanci.
A martanin da ya mayar, Shugaba Ruto ya yi gargaɗi game da tashe-tashen hankali, yana mai jaddada ƙudurin ƙasar na samar da zaman lafiya.
Zanga-zangar ta yau ta zo daidai da rantsar da sabuwar majalisar ministocin Shugaba Ruto, wadda ta ƙunshi ‘yan siyasa hudu na adawa.
Sai dai masu zanga-zangar sun ƙi amincewa da sabuwar majalisar ministocin, saboda shigar da tsofaffin ministocin da ake zargi da “rashin ƙwarewa da rayuwa ta wadaƙa.”
haka kuma akwai wani ƙudurin doka da ke gaban majalisar dokokin ƙasar, wanda idan an zartar da shi, zai dora alhakin duk wata ɓarna a lokacin zanga-zanga kan masu shiryata