Masarautar Kano: Mataimakin gwamna ya nemi afuwar Nuhu Ribadu

Spread the love

Mataimakin gwamnan jihar Kano ya janye kalaman da yi na zargin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro da hannu a rikicin masarautun jihar da ya jawo samun sarki biyu a Kano.

Yayin wani taron manema labarai ranar Lahadi da dare, Aminu Abdussalam Gwarzo ya nemi afuwar Nuhu Ribaɗu yana mai cewa “bai fahimci abin da kyau ba ne”.

“Ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara ya musanta zarge-zargen da muka yi. Na gani a gidajen jarida uku kuma yau [Lahadi] na ga maganar cewa za su kai ƙara kotu,” a cewar mataimakin gwamnan.

“Ya kamata mu bayyana cewa wasu ne suka faɗa mana cewa Nuhu Ribadu ne ke goyon bayan wannan abu tuntuni. Muna neman afuwarsa da ofishinsa game da duk wani abin kunya da hakan ya jawo masa.”

“Dole ne mu amince cewa an fada mana abin da ba haka yake ba game da cewa mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro na da hannu a cikin wannan al’amari”, in ji kwamared Adbulsalam.

A ranar Asabar ne mataimakin gwamnan na Kano, Aminu Abdulsalam ya yi zargin cewa ofishin mai taimaka wa shugaban Najeriya kan tsaro ne ya samar wa sarkin Kano da aka tuɓe wa rawani, Aminu Ado Bayero jiragen sama biyu da suka kai shi birnin Kano tare da samar masa da tsaro.

Lokacin da ya yi bayani ga manema labaru a fadar sarkin Kano da safiyar Asabar, ya ce “Mai ba wa Shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, ya ba da jirage guda biyu, su dakko tsohon Sarki su kawo shi Kano, kuma su kawo shi nan gidan”.

An shiga ruɗani a Kano tun bayan da sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya koma birnin bayan sanarwar tsige shi tare kuma da mayar da sarkin na 14, Muhammadu Sanusi II kan karaga a ranar Juma’a,

Wata kotun tarayya ce ta bayar da umurnin dakatar da aiwatar da dokar masarautar Kano ta 2024, wadda gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.

Kotun ta ce a tsaya a matsayin da ake har sai lokacin da ta saurari ƙarar da aka shigar wadda ke ƙalubalantar dokar masarautar ta 2024.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *