Mataimakin shugaban hukumar kwashe Shara ta Kano ya kama Aiki

Spread the love

Mataimakin shugaban tsaftar muhalli da kauda shara da Adana ta na jahar Kano, Alhaji A. Laminu Muktar Hassan, ya kama aiki a ranar Alhamis 14 ga watan Maris 2024.

Shugaban hukumar kwashe shara ta jahar Kano, Ambasada Ahmad Haruna Zago, ya bayyana cewa ma’ikatar ta samu nasarori na kau da shara a birnin Kano.

Jadawalin gasar Champions League

Sabon mataimakin shugaban hukumar tsaftar muhallin Laminu Mukatar, ya ce gwamnan jahar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf, ya turo shi domin samun hadin kan shugaban hukumar don Samar da ci gaba.

A karshe shugaban hukumar Haruna Zago, ya nemi hadin Kan mataimakin na sa don ciyar da jahar da al’umma gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *