Mataimakin shugaban ƙasar Kenya zai gurfana gaban majalisa

Spread the love

A yau Talata ne mataimakin shugaban ƙasar Kenya zai gurfana a gaban ‘yan majalisar dokokin kasar a birnin Nairobi a ci gaba da yunkurin tsige shi.

Rigathi Gachagua ya bayyana zargin da ake masa a matsayin farfaganda.

Abokan hamayyarsa na siyasa sun zarge shi da cin hanci da rashawa, da zagon kasa ga gwamnati da kuma yada kabilanci.

Mista Gachagua dai ya samu sabani ne da shugaba William Ruto tun bayan tarzomar adawa da gwamnatin kasar a farkon wannan shekara sakamakon shirin karin haraji.

Bayan kada kuri’a a majalisar dokokin Kenya, ana sa ran yunkurin tsige shi zai koma majalisar dattawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *