Kungiyar kananan yan kasuwa ta jihar Kano, karkashin jagorancin Malam Naziru Abdulkadir Da’awa, ta bayyana cewa rashin abun yi ne ke sanya wasu matasa aikata laifuka kamar fadan daba da kwacen waya da makamantansu.
Shugaban kungiyar ya bayyana hakan ne yayin ziyarar godiya da suka kai shelkwatar rundunar yan sandan Kano, karkashin jagorancin kwamishinan ta, CP Ibrahim Adamu Bakori , bisa magance mu su matsalolin da suke fuskanta, a wurare kasuwansu.
Da yake yin Karin haske , kakakin kungiyar kananan yan kasuwar ta jihar Kano, Ibrahim Muhammad, ya ce sunje rundunar yan sandan ne domin ya bawa musu, a matsayin su na kananan yan kasuwa, inda fadan daba yake daga musu hankali har su tafi su bar kayan sana’a’o’in su don tsira da rayukansu, amma bisa jajircewar dakarun yan sandan an magance matsalar da suke fuskanta.
‘’muna ganin yadda kananun yn kasuwa suke shan wahala, suke tiri-tiri sosai da kayansu musamman wajen guje-guje wani ma ya fito da wannan kayan bai kasa ba cikin ikon Allah idan wannan fada ya taso haka zai watsar da kayansa haka kuma wadannan yan daba za su bi su kwashe’’ Ibrahim Muhammad’’.
Sai dai ya kara da cewa an samu nasarar dakile matsalarnan ta guje-guje da kwacen waya, a mahadar kwasuwar Kantin Kwari zuwa Kofar Wambai Kano, domin duk wani abu na aikata laifi ya ragu sosai.
Haka zalika ya ce wannan sabuwar kungiya ce da suka kafa ta don taimakawa jami’an yan sandan, domin su kadai ba za su iya magance matsalar tsaro ba, sai al’umma sun basu goyon baya da kuma hadin kai.
- Katota Ta Kawo Mota Ta SCID Kano Amma Babu Dukiyar Dake Ciki : Barista A.S. Bawa
- Kasa Da Wata Uku Wani Matashi Ya Sake Hawa Saman Allon Talla-tallace A Kano
‘’ misali zan baka lokacin da fitintuna suka yi yawa, a yankunnan mu na Sani Minagge da sauransu muna ganin cewa a wannan lokaci mun yi kokarin yadda za mu mayar da wasu yara kasuwa wadanda kuma basu da aikin yi, a yi kokari a samar musu domin duk masu zare makami su fito fada babban abunda yake kawo hakan rashin aikin yi ne’’.
A karshe ya jinjinawa kakakin rundunar yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa kan yadda yake sauraren jama’a ba a koda yaushe.
Rundunar yan sandan jihar Kano ta bakin mai Magana da yawun ta SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana tabbas wannan kungiya sun yi na’am da ita , bisa yadda suke kokarin ganin an tabbatar da tsaro a fadin jihar.
SP Abdullhi Kiyawa ya kara da cewa kwarin gwiwar da suka basu zai kara musu kaimi wajen gudanar da aiyukansu na kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyinsu.