Matar nan ƴar ƙasar Peru – mai fafautukar taimaka wa mutane wajen kashe kansu, wadda ke tsananin jin jiki a asibiti, ta rasu.
Ana Estrada ta mutu ne bayan da likitanta ya ba ta maganin da ta fiye da ƙima.
Wakiliyar BBC ta ce a cikin wata sanarwa da lauyanta ya fitar, ya ce ta rasu ne ta hanyar da take fata, domin dai tana ta ƙoƙarin ganin ta kashe kanta tsawon shekaru takwas.
Ana Estrada dai ƙwarararriya ce a ɓangaren sanin hallayar dan adam ta kuma yi fama da jinya ta tsawon shekaru.
- Masu Magani Sun Sami Wata Kasuwar A Kano
- Ɓata-gari sun lalata turakun wutar lantarki, sun saka Gombe da Yola da Jalingo cikin duhu