Kungiyar matan jami’an yan sanda ta kasa ( POWA) reshen jahar Kano ta bada tallafin kayan abinci da Kudi ga matan jami’an yan sandan da suka rasa majazensu, domin rage mu su halin radadin rayuwar da ake ciki, bisa jagorancin shugabar kungiyar POWA ta jahar, kuma matar Kwamishinan yan sandan jahar Kano Hajiya A’isha Muhammed Usaini Gumel.
Rabon kayan tallafin ya gudana a wajen shakatawar manyan jami’an yan sanda na Police officers mess dake Unguwar Bompai Kano a jiya Juma’a.
Karanta wannan labarin Gwamnan Kano ya rantsar da sabbin Alƙalai a jihar
Karan ta wannan labarin AIG Umar Sanda ya jinjinawa kwamitin PCRC na jahar Kano
Shugabar POWA, Matar Kwamishinan yan sandan jahar Kano Hajiya A’isha Muhammed Usaini Gumel, ta bayyana cewa sun gabatar da rabon tallafin a Ranar Mata ta duniya, domin tuna wa da irin gudunmawar da suke ba wa al’umma da kuma nuna mu su soyayya, don magance matsalar wariyar launin fata da cin zarafin mata.
An kebe kowacce ranar 8 ga watan Maris na duk shekara, domin bikin murnar nasarorin zamantakewa, tattalin arziki, al’adu da kuma Siyasar Mata.
A’isha Gumel, ta Kara da cewa, sun Yi hakanne domin saukaka mu su radadin rayuwar da aka samu Kai a ciki shi yasa suka zo da tsarin raba kayan abincin, Wanda zai rage mu su radadin da yake damunsu na rashin abincin.
Jaridar Idongari.ng, ta ruwaito cewa, shirin bayar da tallafin an gudanar shi ne karkashin jagorancin matar Babban sufeton yan sandan Nigeria Elezabeth Kayode Abegketun , wadda ta bayar da umarnin tallafa wa matan yan sandan da suka rasa mazajensu.
” Mun tallafa wa Mata 100, insha Allahu za mu Ci gaba da gabatar da wannan tsarin nan bada jima wa ba” cewar A’isha Muhammed Gumel “.
Wadanda suka ci gajiyar tallafin kayan abincin, sun bayyana farin cikinsu sosai, tare da godewa shugaban kungiyar Hajiya A’isha Muhammed Usaini Gumel, wadda ta zamo uwar marayu mai share mu su hawaye a duk lokacin da suke cikin matsala.
Sun Kara da cewa, sun gamsu da yadda A’isha Gumel ta ke tafiyar harkokin kungiyar bisa adalci da gaskiya da rikon Amana domin an ajiye kwarya a inda ya dace.