Matar Mataimakin Gwamnan Neja Ta Rasu

Spread the love

Allah Ya yi wa Hajiya Zainab, matar Mataimakin Gwamnan Jihar Neja, Yakubu Garba rasuwa.

Hajiya Zainab ta rasu ne a asibiti  bayan gajeruwar rashin lafiya.

Mutuwa ta riske ta ne a wani asibiti da ke Minna, babban birnin jihar a ranar Talata.

Gwamnan jihar, Mohammed Umaru Bago, ya bayyana alhini da game da wannan rashi.

Sakon ta’aziyyar da kakakinsa, Bologi Ibrahim, ya sa wa hannu ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga jihar.

Ya kuma yi addu’a Allah Ya sada ta da mafificin rahama a Aljanna Firdausi, Ya ba wa mijinta hakurin jure wannan rashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *