Alhaji Atiku Abubakar (GCON): Wazirin Adamawa shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa ɗaya tilo da yake da dukkan sharuɗɗan da ake buƙata wajen kayar da jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya, idan har da gaske ‘yan adawa na son su karɓi ragamar shugabancin kasa a a kakar zaɓen 2027.
Wazirin Adamawa shi kaɗai ne ɗan gwagwarmaya ɗaya tilo da ya rage a Nijeriya cikin ‘yan siyasa da suke da gogewa da tsari da sanin makamar aiki, wanda ya shafe shekaru a fagen gwagwarmayar siyasa; wanda a kodayaushe yake a ɓangaren neman canji daga mulkin kama-karya zuwa tsantsar dimokuraɗiyya da shugabanci nagari da kuma samar da ci gaba mai ma’ana a ƙasarmu Nijeriya ta ɓangaren tattalin arziki da inganta tsaro.
Atiku shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa ɗaya tilo a babbar jam’iyyar adawa ta PDP da yake tare da manyan jiga-jigan ‘yan siyasar ƙasa da suke da ƙwarewa wajen sanin gwamnatin tarayya, shi ne wanda ya ɗauki tsawon shekaru sama da 20 yana fafutuka ta hanyar sadaukarwa da jajircewa da ƙoƙarin samar da tsabtatacciyar dimokiraɗiyya a Nijeriya.
Kwarewar Siyasa da da Alhaji Atiku Abubakar yake da ita tana da girma sosai, ta dalilin haka ne ma yake da farin jinin jama’a da kuma wanda karansa ya kai tsaiko da ya isa ya doke gwamnati da jami’iyya mai mulki saboda ƙwarewarsa da tasirinsa a fagen siyasa.
Alhaji Atiku Abubakar (GCON): Wazirin Adamawa ya yi daidai da yanayin siyasar Nijeriya fiye da duk wani mai son tsayawa takara daga manyan jam’iyyun siyasa biyu masu ƙarfi, saboda haka ne ma ya zama ya samu karɓuwa ta musanman a wurin jama’a irin wadda babu wani ɗan siyasa a Nijeriya da ya samu irinta a tsawon wannan lokaci na mulkin dimokraɗiyya tun daga shekarar 1999 zuwa yau.
Mai girma Wazirin Adamawa, mutum ne da ya samu shaidar ƙwarewar aiki da kyakkyawar mu’amilla da jama’a ta fuskar harkokin siyasa da hulɗar kasuwanci da zamantakewa da kuma kishin ƙasa, uwa-uba da rungumar kowane ɗan Nijeriya ba tare da nuna wani ɓangarenci ko nuna wariyar launin fata ko ƙabilanci ko bambancin addini ko yankin da mutum ya fito ba a duk faɗin Nijeriya.
Waziri yana da kyakkyawar niyya da ƙudurin samar da gyara da haɗin kai a tsakanin ‘yan Nijeriya, da tabbatar ɗorewar mulkin dimokaraɗiyya ta hanyar rainonta zuwa babban mataki. Waziri wani jigo ne a siyasa mai girman gaske, wanda ya kafu ya kuma tsallake dukkan wani tarko da aka ɗana masa don tatsile kokarinsa na tabbatar da dimokiraɗiyya saboda kasancewarsa jigo kuma tsayyayye a koyaushe a da’irar siyasa da ya karaɗe ko’ina a duk faɗin Nijeriya.
Alhaji Atiku Abubakar ya kasance Mataimakin Shugaban Nijeriya mai biyayya a tsawon shekaru takwas da ya kwashe a wancan lokacin, shi kansa wancan shugaban ya yi nasarar hawa kan kujerar ne ta hanyar kungiyar siyasa ta Turaki, kuma an yi gagarumar nasarar a ƙarƙashin inuwar Alhaji Atiku Abubakar da jagorancinsa har karo biyu a jere, sannan ya zama guda cikin waɗanda suka fatattaki shugaban ƙasa na wancan lokacin (Olusegun Obasanjo) a lokacin da ya yi niyyar dawwamar da kansa a kan kujerar mulki, wanda hakan ya saɓa da kundin tsarin mulkin Nijeriya da kyawawan dabi’u nagartattu. don haka shi ma tsohon shugaban ya amfana da irin nagartar Atiku da ƙwarewarsa da kyawawan ɗabi’unsa ababan koyi da nagarta.
BABBAR ALAMAR DIMOKRAƊIYYAR NIJERIYA ƊAYA RAK ATIKU NE
Wazirin Adamawa shi ne shaida ko alama mafi girma a tsarin tafarkin dimokuraɗiyya a wannan lokacin da muke ciki, saboda irin juriyarsa da tsallake ƙalubale da dama da Irin sadaukarwarsa da ya bayar wajen tabbatuwar ɗorewar dimokiraɗiyya a Nijeriya tun daga haihuwarta da ci gaba da rainonta zuwa wannan lokacin na matakin da take kai a yanzu
Tsarin siyasa dimokuraɗiyya a Nijeriya ba tare da irin gudummawar Alhaji Atiku ba lami ne, abu ne mara tasiri wanda ba zai bayar da wata ma’ana ba. Atiku shi ne alama kuma shaida kazalika kuma babban kwamandan kwamandoji jarumai ‘yan gwagwarmayar siyasa dimokuraɗiyya a wannan lokacin, saboda babu wani mataki ko wata nasara guda ɗaya da aka cimma a tsarin siyasar Nijeriya ba tare da kwazonsa da irin gudummawarsa da ya bayar ba.
Na farko yana cikin manyan jagorori waɗanda suka kafa jam’iyyar PDP, wanda ya jagoranci haɗin kan ‘yan Nijeriya, kuma wannan na ɗaya daga cikin abu mafi girma a tarihin Nijeriya tun daga lokacin kafa Jamhuriya ta farko zuwa yau.
Burin Alhaji Atiku Abubakar na farko shi ne ya zama Gwamnan Jiharsa ta Adamawa, wanda a wancan lokacin an zabe shi bayan ya cika dukkan ka’idojin cin zaɓe kafin Allah ya yi ikonsa ya ƙaddara masa zama kan kujera ta biyu a muƙamin Mataimakin Shugaban Ƙasa.
Waziri ya na da cikakkiyar dama da zai iya zama Shugaban ƙasa a shekarar 2003, amma irin karamcinsa da biyayyarsa da irin kishin ƙasa irin na Alhaji Atiku Abubakar ya hana shi tunkarar kujerar, har sai lokacin da tura ta kai bango lokacin da tsohon Shugaban Nijeriya Obasanjo ya so yi wa tsarin kundin mulki karan-tsaye, sanan ya bijire masa ta hanyar daƙile buƙatarsa ta cin amanar ƙasa.
Na farko dai Atiku yana cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar PDP wanda ya kafa tarihi a Nijeriya tun daga Jamhuriya ta farko.
Burinsa na farko shi ne ya zama Gwamnan Jiharsa ta Jihar Adamawa kuma an zaɓe shi bisa cika dukkan ƙa’ida kafin ƙaddara ta kai shi matsayi na biyu a matsayin mataimakin shugaban kasa.
Alhaji Atiku Abubakar ya samu damarmarki da dama da zai iya tunkarar zama Shugaban ƙasa a shekarar 2003, amma irin karamcinsa da biyayyarsa da kishin ƙasarsa ya sa Atiku ya haƙura bai nuna buƙatar hakan ba, har sai da lokacin da tsohon Shugaban ƙasa Obasanjo ya so ya yi wa kundin tsarin mulki karan-tsaye, sannan Waziri ya dakatar da shi, ya taka masa burki ta hanyar daƙile shirinsa na cin amanar ƙasa da karya ƙa’idodin kundin tsarin mulkin ƙasa.
Atiku ya ci gaba da gudanar da rayuwarsa har zuwa ƙarshen wa’adin mulkin su na biyu a matsayin mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar adawa wanda shi ne rikicin siyasa mafi girman gaske da ya samu kansa ciki, an sha shari’o’i da ƙalubale da dama.
Atiku shi ne babban abin koyi da kwaikwayo a fagen gwagwarmaya a dimokuraɗiyyar Nijeriya, wanda babu wata barazana da ta yi masa tarnaƙi ko barazanar ɗauri da ta saka ya yi gudun hijira zuwa ƙasashen waje tun daga lokacin da ya fara gwagwarmayar dimokuraɗiyyar neman ‘yancin zuwa yau. Kowa gamsu kuma ya yi amanna cewa mafarkinmu da burinmu na dimokuraɗiyya shi ne samar da ci gaban tattalin arziƙi da inganta batun tsaro da samar da hulɗar diflomasiyya da muka cancanci mu samu a matsayinmu na babbar ƙasa a Afirka.
Atiku shi ne mafi dacewa kuma mafita wurin warware ɗimbin matsalolin Nijeriya da suka haɗa da tabarbarewar tattalin arziki da magance rikice-rikicen siyasa da ƙalubalen tsaro da rashin martaba mu a cikin ƙasashen duniya. Shi ne mutum mafi dacewa da Nijeriya da ya dace a tasa a gaba don ciro kitse daga wuta.
Shugabancin Alhaji Atiku Abubakar zai bayar da mamakin da ba a zata ba, kuma ba na son rai ko nuna ɓangaranci ba, saboda duk waɗancan matsalolin da suka addabi Nijeriya za su zama tarihi a Nijeriya. Sannan Nijeriya za ta ɗaga darajarta a idon duniya har wasu suke sha’awarmu da girmama mu.
Irin soyayyar Alhaji Atiku da iliminsa da damuwarsa kan lamuran Nijeriya, babu shakka ya zarta duk wani mai neman shugabancin Nijeriya.
Nijeriya gida ce a wajen Atiku; Da zarar mun ba shi dama za mu samu abin da muke fata da burin samu cikin ƙanƙanin lokaci a matsayinmu na ƙasa ɗaya kuma al’umma ɗaya.
Nagode da fatan Allah ya saka da alheiri!!!
Com. Bashir Suwaid
Jagoran Ƙungiyar,
PDP Jirgin Fiton Al’umma 2027