Matashi Mai shaidar karatun NCE ya rungumi sana’ar sayar da rake a Kura

Spread the love

Wani Matashi mai shaidar karatun NCE, Mai suna Muhammed Muhammad Brigade, ya rungumi sana’ar siyarwa da matse ruwan rake da inji a kura ga mabukata.

A hirarsa da Idongari.ng , Muhammad ya ce ya rungumi sana’ar ne a kokarinsa na ganin ya dogara da kansa.

Ya ce gabanin fara sana’ar ya nemi shawarar mahaifan sa inda suka sa masa albarka da karfafa masa gwiwar ya rike sana’ar da hannu biyu.

A cewar sa ya fuskanci suka daga abokanai da ‘yan uwa kafin samun karfin gwiwar ya fara sana’ar wanda yanzu haka yake taimaka wa da dama daga cikin ma su hana shi rungumar sana’ar tunda fari.

“Da farko bayan ware kudin damin rake dana kura da wuka da sauran kayayyaki, na sanya kudi naira dubu 90, na sayi injin matse ruwan raken kirar kasar chana don inganta sana’ata, wanda yanzu haka kudinsa ya koma naira dubu 160-“inji Muhammed Muhammad.

Ya ce a kowacce rana yana samun ribar naira dubu 8 zuwa sama duka a dalilin ajiye girman kai wajen riko da karamar sana’a, wanda yake da dimbin abokanan huldar da wasu ma ba ‘yan Najeriya bane ba.

Daga karshe ya shawarci matasa da su riki sana’a komai kankantar ta domin kauce wa haduwa da matsalar jirkicewar tunani da mutuwar zuciya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *