Matashi ya mutu ana cikin tafiya a motar haya

Spread the love

Wani matashi dan shekara 29 ya yanke jiki a fadi a mace a lokacin da suke tsaka da tafiya a cikin motar haya a Jihar Ogun.

Matashin mai suna Anuoluwapo Aderemi, ya rasu a cikin bas din ne cikin dare, a lokacin da suka tsaya shan mai a wani gidan mai a yankin Itori.

Rundunar ’yan sanda da ke Jihar Ogun ta ce ya rasu ne hanyarsu ta zuwa Ibadan,  babban birnin jihar Oyo, daga Papalanto a Karamar Hukumar Ewekoro.

Kakakin rundunar, Odutola Omolola, ta ce direban motar ne ya sanar da su game da rasuwar matashin a cikin bas dinsa mai dauke da fasinjoji daga Papalanto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *