Matashi Ya Rasu Bayan Hana Masu Kwacen Waya Aikata Laifi.

Spread the love

Iyayen matashinan mai suna, Nura Abubakar, da ya rasu sanadiyar wasu batagarin matasa da suka afka masa da sara, saboda ya yi musu magana bayan sun kwace wayar wata budurwa, sun bukaci mahukunta su yi adalci wajen gano wadanda ake zargin tare da hukunta   su.

Marigayin ya rasa ransa ne, a ranar asabar din data gabata da  magariba, lokacin da ake dawo wa daga zagayen Takutaha, a yankin unguwar Kwanar Dala dake Kano.

Alhaji Abubakar Umar, shi ne mahaifin marigayin ya bayyana cewa, yana zaune a kofar gida aka sanar da shi cewa , an halaka masa dansa, inda lamarin ya gigita shi saboda yasan baya rigima da kowa.

Ya kuma yi kira ga gwamnati dama hukumomin tsaro su dauki tsattsauran mataki na bankado wadanda ake zargin tare da hukunta su, domin ba za su yafe zibda jinin dansu da batagarin matasan suka yi ba.

Wani dan uwan marigayin ya shaidawa jaridar Internet ta www.idongari.ng,  cewa lokacin da abun ya faru suna tare dashi, kuma sun yi masa haka ne saboda ya yi musu Magana don su daina kwacen wayoyin jama’a, inda nan take suka afka masa wasu suna saran sa yayin da sauran kuma suke sukarsa da wukake.

Ya kara da  cewa akalla matasan da suka afkawa marigayin sun kai 20, kuma sun gane hudu daga cikinsu .

Sai dai sun ce bayan an kawo gawarsa sai da wasu daga cikinsu batagarin suka zo har gida don su tabbatar ya rasu.

Shakikan Marigayin sun kara da cewa , sun bayyana wa jami’an yan sanda faruwar lamarin kuma sun fara gudanar da bincike.

Wakilin mu ya yi kokarin jin ta bakin mai Magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, amma hakan bata samu ba.

Yanzu haka ana gudanar da zaman makokin Nura Abubakar Umar ,  a unguwar Chediyar Yan-Gurasa dake jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *