Matashi Ya Shiga Hannu Kan Lalata Taransifoma A Adamawa

Spread the love

Hukumar Tsaro ta Sibil Difens a Jihar Adamawa, ta kama wani matashi mai shekara 24, Auwal Sale, kan zarginsa da hannu wajen lalata na’urar taransfoma da kuma satar mai.

Kwamandan hukumar a jihar, Ibrahim Mainasara, ya ce an gano wanda ake zargin yana da galan 10, wanda huɗu daga ciki ke ɗauke da man taransifoma.

Ya ce ana zargin ya haɗa kai da wasu mutane, ciki har da wani mai suna Daddy, wanda ta tsere wajen aikata laifin.

A cewarsa, yayin bincike rundunar ta gano wani mutum da ake kira Alhaji, daga ƙaramar hukumar Song na da hannu wajen sayen man da suke satowa.

Ya ce da zarar sun kammala bincike za su miƙa wanda ake zargin zuwa kotu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *