Matashin Da Inji Ya Kama Wa Hannu Ya Yi Karar Kamfanin ASPIRA

Spread the love

Wata kotun ma’aikata ta kasa dake Kano wato National Industrial Court, ta fara sauraren karar da Malam Muhammad Umar Adamu, ya shigar da kamfanin ASPIRA don neman hakkinsa .

Muhammad ya shigar da karar ce ta hannun lauyansa, Barister Badamasi Tijjnani Gandu.

Tunda farko mai karar wanda dalibi ne a jami’ar Aliko Dangote Kano, ya nemi aiki a kamfanin ASPIRA don dogaro da kansa, kuma lokacin da yake gudanar da aikinsa inji yakama masa hannu, har sai da aka yanke masa hannun dama.

Mai karar ta hannun lauyansa Barista Badamasi Sulaiman Gandu, ya nemi a biya shi diyar naira dubu dari uku da dari biyar da ashirin da biyu (300,522,000) da kuma hannun Roba mai motsi (Biometric Hand).

Sai dai bayan shigar da wannan roko ne kotun ta bayar da damar yin sulhu tsakanin kamfanin da kuma mai karar.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *