A safiyar Talata Matatar Man Ɗangote ta fara fitar da rukunin farko na tataccen man fetur.
Matatar Ɗangote mai karfin samar da ganga 650,000 na tataccen mai a kullum ta fara fitar da fetur ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalarsa da kuma fargabar tashin farashinsa.