Matatar man fetur ta Dangote za ta sayi ganga miliyan 24 na ɗanyen mai daga Amurka

Spread the love

Matatar mai ta Dangote na shirin sayo aƙalla ganga miliyan 24 na ɗanyen man fetir daga Amurka nan da shekara mai zuwa domin ƙarfafa ayyukan matatar.

Cikin wani rahoto da jaridar Bloomberg ta fitar, ya nuna cewa matatar man fetir ɗin ta gabatar da buƙatarta nasayen ganga miliyan biyu a kowane wata daga kamfanin dilklancin man fetur na ‘West Texas Intermediate Midland’ har na tsawo wata 12 da za a fara daga watan Yuli, wanda hakan zai sa matatar ta sayi ganga miliyan 24 a tsowan shekarar.

Buƙatar neman man fetur daga Amurka na nuna irin fama da ƙarancin tono mai da ƙasar ke fama da shi, tare da nuna irin tasirin da matatar za ta yi a kasuwan man fetur ta duniya, da zarar ta fara aiki.

Najeriya dai ta kasa cimma kason da ƙungiyar OPEC ta ware mata na yawan man da za ta fitar na aƙalla shekara guda.

A watan Afrilu ƙasar ta riƙa tono kusan gangar mai miliyan 1.45 a kowace rana, abin da ya yi ƙasa da kason da OPEC ta ware wa ƙasar na ganga miliyan 2.6 a kowace rana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *