Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ɗora alhakin ƙarancin man fetur da ake samu a Najeriya kan dillalan man da ya ce ba su saya daga gare shi.
Dangote ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da kwamitin shugaban ƙasa kan sayar da ɗanyen man fetur a Naira ga kamfaninsa.
Sannan a wani ƙarin bayani da ya yi, wanda tashar Channels ta ruwaito, ya ce, “mun ƙiyasta cewa Najeriya na buƙatar lita miliyan 30 zuwa 32 a kullum. Wannan ba matsala ba ce saboda yanzu haka muna da lita miliyan 500 a tankinmu, wanda ke nufin ko ba mu tace wani man ba, muna da man da zai wadatar da Najeriya na sama da kwana 12,” in ji Ɗangote.
Ya ƙara da cewa a shirye matatarsu take ta samar da lita miliyan 30 ga ƴan Najeriya.
“Ina so NNPCL da sauran dillalan mai su daina shigo da man fetur, su zo wajenmu su saya. Amma idan suka zo suka saya man a matatarmu, za a daina ƙarancin man da ma dogon layi a gidajen mai.”