Kamfanin jirgin sama na British Airways ya hana fasinjoji 58 hawa jirginsa da zai tashi daga Abuja zuwa Landan saboda matsala da ƙofar jirgin ta samu.
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA), ta ce kamfanin jirgin ya bar wasu kujeru babu kowa saboda dalilan tsaro.
Daraktan Yaɗa Labarai da Kare Haƙƙin Fasinjoji na NCAA, Mista Michael Achimugu, ya wallafa a shafinsa na X cewa matsala ce ta sa aka hana fasinjojin hawa jirgin.
Ya ce an bai wa fasinjoji 30 wajen kwana a wani otel, yayin da 28 suka koma gidajensu.
Dukkanin fasinjojin da abin ya shafa za su iya neman haƙƙinsu, kuma kamfanin yana shirin jigilar su a ranar Asabar.
- Rundunar Yan Sandan Kano Ta Haramtawa Karota Bayar Da Tsaro A Zaben Cike Gurbi
- Wasu Batagari Sun Farmaki Gidan Malamin Isilamiya Cikin Dare A Kano
Achimugu, ya kuma shawarci matafiya su riƙa neman jami’an Kare Haƙƙin Fasinjoji na NCAA a filin jirgi idan aka samu jinkirin tashi, domin tabbatar da cewa an kare haƙƙinsu.
Wasu mutane a shafukan sada zumunta sun buƙaci NCAA ta duba yanayin jirage da wasu kamfanonin ƙasashen waje ke kawo wa Najeriya.
Sun bayyana cewa kuɗin tikitin da fasinjoji ke biya ya yi yawa, kuma duk da haka jiragen ba su da cikakkiyar lafiya.