Matsalar Ruwan Famfo a karamar Hukumar Tudun wada Tazo karshe: Shugabar Karamar Hukumar Tudun wada.

Spread the love

 

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo

 

Bayan rantsar da shugabar ƙaramar hukumar Tudunwada, Hajiya Sa’adatu Salisu Soja, ta kai koken al’ummar karamar Hukumar Tudun wada ga mai girma Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, akan matsalar Ruwan famfo dake damun al’ummar yankin.

Haj Sa,adatu tace ba iya matsalar ruwan ke damun alummar ba harda aikin titina na tsawon kilometer 5 da akeyi a kananan hukumomin jihar kano duk a kokarinta na ganin ta kawo cigaban raya kasa a wannan karamar hukuma.

Shugabar karamar hukumar Hajiya Sa’adatu Salisu Yushau Soja ta bayyana hakan ne ayayin data kai ziyarar gani da ido gidan Ruwan Tudun wada.

Inda ta karada cewa takai wannan ziyara ne, domin ganin halin da gidan yake ciki da kuma matsal tsalun da suke damun gidan ruwan, wanda wannan ziyara umarni ne daga mai girma Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da suje da ma’aikata a gani mecece matsalar da tasa al’ummar Tudunwada basa samun Ruwan sha? Wannan ya faru ne bisa jajircewar ita shugabar karamar hukumar.

“Cikin ikon Allah ma’aikata har sun zo daga ma’aikatar aiyuka ta Jihar Kano, kar kashin jagorancin kwamishinan aiyuka na jihar Kano domin duba halin da dükkan wannan gurare suke ciki

Ta kuma bada umarnin da a biya dukkan ma’aikatan wucin gadi (Temporary da Messengers) da aka dade ba’a biyan su hakkın su kuma tace ashirye take domin cigabada bijiro da managartan ayyukan dazasu kawowa Alummar Tudun wada cigaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *