Matsalar Satar Mutane Ma su Yawa ta sake Kunno Kai A Nigeria

Spread the love

Matsalar satar mutane masu yawa sosai ta sake kunno kai a Najeriya.

Sau biyu a cikin mako guda, wani gungun ‘yan bindiga da ke kan babura, da suka fito daga dazuka a wurare biyu daban-daban a arewacin kasar, suka yi awon gaba da daruruwan mutane.

Na farko shi ne al’amarin da ya faru a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda mayaka da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka yi awon gaba da mata da yara kanana daga wani sansanin ‘yan gudun hijira a lokacin da suke neman itacen girki.

Sai kuma al’amarin da ya faru da safiyar ranar Alhamis inda ‘yan bindiga suka yi awon gaba da yara fiye da 280, masu shekaru tsakanin 8 da 15, da kuma wasu malamai daga wata makaranta da ke jihar Kaduna da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya zuwa wani daji da ke kusa.

Akwai rahotanin cikin gida da ke cewa mayakan kungiyar Ansaru mai alaka da al -Qaeda ce suka kai wannan harin.

Matar Kwamishinan Yan Sandan Kano Ta Tallafawa Membobin POWA 100.

An Sauya Wa Ma’aikatan Kano Lokutan Aiki Albarkacin Watan Ramadana

A watannin baya-bayan nan, an samu matukar raguwa kan batutuwan da suka shafi satar mutane masu yawa sosai, wadda matsala ce da ta rika addabar wasu yankunan kasar tun bayan ‘yan matan makarantar sakandiren Chibok su kusan 300 da aka sace a watan Afrilun 2014 wanda ya rinka jan hankalin kafafen watsa labaran kasashen duniya.

Sai dai a yanzu matsalar ta sake kunno kai yayin da ake shirin cika shekara 10 da faruwar al’amarin .

A cikin batutuwan da suka shafi mutane masu yawa sosai da aka sace a jihar Kaduna na daliban Kuriga shi ne mafi girma tun bayan 2021.

To ko me ya sa ake sake samun bullar matsalar masu garkuwa da mutane da ke jefa rayuwar yara cikin hadari?

Abu ne mai wuya a iya tantance dalilan da suka sa wadannan al’amura biyu da ba su da alaka da juna suka faru kusan lokaci daya sai dai tunatarwa ce cewa barazanar ba ta tafi ba.

Sai dai a bayyane take cewa al’amuran sun faru ne yayin da ake shire-shiryen fara azumin Ramadan.

Wadanda aka yi awon gaba da su a baya kuma aka sakosu sun yi magana a kan yadda aka rika tilasta mu su yin girki tare da wasu ayyuka a sansanonin ‘yan bindigar da ke cikin daji.

Sai dai a bayyane take cewa satar mutane domin neman kudin fansa a Najeriya wata harka ce da ke gudana cikin sauki wadda kuma take bada damar samun kudade masu yawa .

Ana sakin wadanda aka yi awon gaba da su ne bayan an biya kudin fansa, kuma ba kasafai ake kama wadanda suka aikata laifin ba.

Hakan kuwa na faruwa ne duk da cewa an haramta biyan kudin fansa.

A takaice mutane fiye da 4,700 aka yi garkuwa da su tun bayan hawan Shugaba Bola Ahmed Tinubu hawa mulki a watan Mayun bara a cewar cibiyar da ke tattara bayanan sirri ta SBM.

Satar mutane dai ta koma wata harka ta samun kudi da jama’a wadanda suke son su tara kudi ta kowace hanya.

Bayan neman kudin fansa, ‘ yan bindigar a baya sun bukaci a ba su kayan abinci da babura har ma da man fetur domin su saki mutanen da suke garkuwa da su.

” Matsalar matsin tattalin arziki a Najeriya ta haifar da yanayin garkuwa da mutane. Tun daga shekarar da ta gabata, gwamnatin kasar ta kasa shawo kan matsalar da ake fuskanta a kasuwar mussayar kudade ta kasashen waje” a cewar William Linder, wani tsohon jami’in hukumar leken asirin Amurka watau CIA wanda kuma shi ne shugaban wata cibiya da ake kira 14 North.

“Farashin abincin ya yi tashin gwauron zabo musamman a cikin watanni shida da suka gabata. Kawo yanzu ana ganin matsalar cin hanci da rashawa ba ta sauya zani ba ,” in ji shi.

Shi ma Alex Vines, wanda shi ne daraktan sashin kula da kasashen Afrika na Chatham House na da ra’ayi irin wannan:

”Za a iya danganta hare -haren baya baya nan a kan durkushewar tattalin arzikin kasar da kuma rashin daukar kwararan matakan tsaro da za su dakile ayuikan ‘yan bindigar” in ji shi

Hauhawar farashin abinci ya ta‘azzara ne saboda manoma ba sa samun damar zuwa gonakinsu saboda suna tsoron ‘yan bindigar za su iya kai mu su hari ko kuma su sace su

Dr Vines ya bayyana cewa:

” A yankuna da dama gungun ‘yan bindiga sun maye gurbin gwamnati da sarakunan gargaji a matsayin hukuma’’.

‘Yan bindigar na yawan karbar kudi daga hannun mutane amma kasancewar ba sa iya noma na nufin cewa za su fuskanci karancin kudi watakila wannan na cikin dalilan da suka sa ‘yan bindigan suka koma yin garkuwa da mutane masu yawa sosai.

Haka kuma janyewar tafkin Chadi da kwararowar hamada a kudanci sun sa ana fuskantar karancin filin noma da kuma Ruwan sha.

“Wannan matsala ta kara jefa mutane da yawa cikin wahala musaman a arewacin kasar. Wannan ya sa mutane su na neman wasu hanyoyin samun kudin shiga. Abin takaici, satar mutane don neman kudin fansa na ciki ,”in ji Mista Linder.

Haka kuma ‘yan bindigar na cin karensu babu babbaka saboda rashin jami’an tsaro a kan iyakokin kasar. Haka kuma matsalar mayaka masu ikirarin jihadi a yankin ta kara janyo tabarbarewar tsaro.

‘Yan bindigar sun maida dazuzzukan da kann iyakokin kasar zuwa sansanonin ma su aikata miyagun laifuka

“Akwai bukatar ganin cewa Najeriya ta yi aiki tare da makwabtanta. Idan babu hadin kai tsakaninta da Nijar da Kamaru da Chadi da kuma kan iyakar kasar da ke yankin arewa maso yammacin kasar, to wadannan al’amura za su ci gaba da maimata kansu,” in ji Bulama Bukarti, wanda jami’i ne a cibiyar Tony Blair.

Malam Bukarti ya kara da cewa hakan kadai ba zai taimaka wa Najeriya wajen murkushe ‘yan bindigar ba.

Akwai bukatar ganin cewa mahukunta sun gurfanar da su gaban kuliya.

“Ba mu taba ganin an kama jagoran ‘yan bindigar ba tare da gurfanar da shi gaban kuliya.

Sana’a ce da ake samun riba. A don haka za a samu karin mutane da za su shiga cikin wannan harka kuma rashin hukunci zai karu,” in ji shi.

BBCH

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *