Matsalar Tsaro Ta Sake Dawowa A Bauchi

Spread the love

Kasar Hakimin Lame da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi yanki na cikin yankuna mafiya girma da tarin jama’a a karamar hukumar da jihar.

Yankin ya yi iyaka da jihohin Kaduna da Filato da Kano da Yobe, da kuma dajin Lame- Burra da Falgore.

A kwanakin baya matsalar tsaro ta yi kamari a yankin har ta jawo wasu mutane suka fara kaura zuwa cikin garin Bauchi da wasu garuruwa.

Aminiya ta ruwaito yadda Hakimin Lame, Sarkin Yakin Bauchi, Alhaji Aliyu Yakubu Lame ya hada hannu da maharba da jami’an tsaro da taimakom Gwamnan Jihar Bauchi da Karamar Hukumar Toro wajen shiga cikin dajin da kauyuka inda suka kori ’yan ta’addar.

Sai dai a makon jiya, ’yan bindiga sun yi garkuwa da mutum uku ciki har da wata mace tare da kashe Sarkin Ririwai, Alhaji Garba Badamasi bayan sun sace shi daga fadarsa a Gundumar Lame da ke Karamar Hukumar Toro.

Hakimin Alhaji Aliyu Yakubu Lame ya tabbatar da faruwar hakan lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan lamarin, inda ya ce abin takaici ne yadda ayyukan ’yan bindigar ke kokarin damowa a yankinsa.

Sarkin Yakin ya ce, masu garkuwa da mutanen da farko sun yi garkuwa da mutum uku ciki har da wata matar aure, kafin su je su dauki sarkin a fadarsa, bayan sun yi masa duka, ya samu raunuka da dama a kan hanyarsu ta zuwa maboyarsu, wanda aka ce sakamakon raunin da ya samu ne ya kasa tafiya, sai suka kashe shi, suka jefar da gawarsa.

Sarkin Yakin ya ce, kwana biyu kafin su je gidan sarkin, sun je gidan wani matashi don su sace shi, suka kasa karya kofarsa, sai suka fasa masa katanga kafin su iya shiga, suka dauki matarsa, aka aika musu da Naira miliyan hudu, suka amsa, sannan suka rike wanda ya je kai kudin.

Gwamnan Kano ya yi watsi da yadda tsarin raba abincin azumi a jihar

Ɗalibai Tsangaya 15 da aka sace a Jihar Sakoto sun shaki iskar yanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *