Fitaccen marubucin waƙoƙin Hausa da na siyasa, Garba Gashua ya rasu.
Babban ɗan marigarin, Musa Garba Gashua ne ya tabbatar wa BBC rasuwar tsohon mawaƙin, wanda ya rasu a ranar Lahadi da asuba, yana da shekara 73 a duniya.
Garba Gashua ya yi fice a waƙoƙin siyasa musamman a lokacin jamhuriya ta uku a Najeriya, daga zamanin mulkin Babangida zuwa lokacin siyasar SDP da NRC.
Tuni aka yi jana’izar marigayin – wanda ya mutu ya bar ‘ya’ya 11 da jikokki da dama.