MawaƙiyaTaylor Swift ta shiga jerin waɗanda suka fi kowa kuɗi a duniya

Spread the love

Mawaƙiya Taylor Swift ta shiga sahun Elon Musk da aka bayyana su cikin jerin mutanen da suka fi kowa kuɗi, a duniya, a cewar sabon jadawalin masu arzikin duniyar.

Mawaƙiyar ta shiga jerin masu arzikin duniya na mujallar Forbes a karon farko da dala biliyan 1.1 tare da Sam Altman wanda ya ƙirƙiri manhajar ƙirƙirarriyar basira ta ChatGPT wanda yake da dala biliyan ɗaya.

Bernard Arnault wanda ke da kamfanin LVMH da ke ƙera abubuwan ƙasaita da iyalinsa sune kan gaba da arzikin dala biliyan 233.

Forbes ta ce 2024 ta kafa tarihi inda aka samu mutane 2,781 cikin jerin masu arzikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *