Mayaka 400 Sun Mika Wuya A Nijar

Spread the love

Sama da mayaƙa 400 da suke addabar yankunan arewacin jamhuriyar Nijar ne suka miƙa wuya a birnin Agadez, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasar, ANP ta ruwaito.

Rahoton ya ƙara da cewa mayaƙan ƴan ƙungiyar Patriotic Liberation Front da Movement for Justice and Rehabilitation of Niger ne.

An ce mayaƙan sun amince da kiran shugaban ƙasa Janar Abdourahmane Tchiani na miƙa wuya ne.

Ba a taɓa samun mayaƙa da suka kai wannan adadin ba, sannan a ranar 3 da 11 ga watan Nuwamba ma an samu irin hakan, inda wasu mayaƙan daban suka miƙa wuya a birnin na Agadez.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *