Mazauna Geidam na zargin tubabbun ‘yan Boko Haram da yi musu barazana

Spread the love

Al’ummar yankin ƙaramar hukumar Geidam ta jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya sun ce suna cikin matsananciyar fargaba tun bayan da gwamantin jihar ta tsugunar da wasu tubabbun ‘yan Boko Haram.

Mutanen sun zargi tsoffin mayaƙan Boko Haram ɗin da suka ajiye makaman da hana su zuwa gona da yi musu ƙwace tare da yawo a makamai a cikin gari.

Wasu daga cikin al’ummar yankin dai sun shaida wa BBC cewa tun bayan da gwamantin jihar ta Yobe ta tsugunar da tubabbun mayaƙan Boko Haram da suka tuba a yankunansu, suka shiga ɗar-ɗar, kan yadda suke matsa musu tare da jefa faragaba a zukatansu.

”Mata da yara da waɗanda ke zuwa cin kasuwa na fuskantar barazana daga waɗannan mutanen, duk da damina ta sauka amma har yanzu suna faragabar zuwa”, kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC.

Shi ma wani mazaunin yankin da BBC ta zanta da shi, ya ce tubabun y’an boko haram din na yawo ne da makamai, wanda hakan ke kara jefa su cikin barzana.

To sai da gwamnatin jihar Yobe ta musanta wannan iƙirari, kamar yadda mai bai wa gwamnan jihar shawara kan kan harkokin tsaro, Brigadiye Dahiru Abdusalam mai ritaya ya bayyana.

Ya ce su waɗannan tubabbun mayaƙan Boko Haram suna rayuwa ne ƙarƙashin kulawar sojoji, kuma suna taimaka wa jami’an tsaron wajen yaƙin da mayaƙan Boko Haram ɗin.

”Don haka wannan iƙirari da mazauna yankin suka yi ba gaskiya ba ne, saboda har kuɗi muke biyan mutanen nan kan aikin da suke yi mana wajen yaƙi da Boko Haram”, in ji mashawarcin gwamnan.

Garin Gaidam na jihar Yobe na daga cikin yankuna a jihar Yobe da ke fama da matsalar Boko Haram, wanda ko a wattanin da suka gabata sai da wasu mayaƙan suka kai hari yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *