Dan wasan gaban Faransa Kylian Mbappe ya sanar da cewa zai bar PSG a karshen kakar wasanni ta bana.
Mbappe mai shekara 25 ya sanar da wannan mataki ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
“Kullum ina fada cewa zan tattauna da ku idan lokacin hakan ya zo,” in ji Mbappe.
“Wannan ce shekarata ta arshe a PSG. Ba zan ƙara tsawaita kwantaragi ba, komai zai zo ƙarshe nan da ‘yan makonni.”
Kwantaragi tsakanin PSG da dan wasan za ta kare ne a watan Yuni, kuma a watan Fabirairu BBC ta ruwaito dan wasan zai koma Real Madrid a kakar wasanni mai zuwa.
Dan wasan da ya lashe kofin duniya shi ne ya fi kowa cin kwallaye a tarihin kungiyar ta PSG inda yake da kwallo 255.