Me Ya Sanya Hukumar Zaben Kano Sauya Ranar Zaben Shugabannin Kananan hukumomin.

Spread the love

Hukumar zabe Mai zaman kanta ta jihar Kano ta sauya lokacin gudanar da zaben kananan hukumomin jihar zuwa watan oktoba 2024.

Kadaura24 ta rawaito Shugaban hukumar faefesa Sani Lawal Malunfashi ne ya sanar da haka yayin Taron masu ruwa da tsaki a Shelkwatar hukumar.

DANDALIN KANO FESTIVAL

Shugaban hukumar zaben ta jiha ya ce za a fara yakin neman zabe daga ranar 1 gq watan satunba 2024 , sai Kuma zabukan fitar da gwani daga jam’iyyu daga ranar 3 zuwa 14 ga watan satunba yayin da Kuma za a fara sayar takardun neman tsayawa takara ranar 15 ga watan satunba zuwa 26 ga watan satunba.

Farfesa Sani Lawal Malunfashi ya ce za a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar Kano da kansilolin su ranar Asabar 26 ga watan oktoba na wannan shekara yayin da hukumar za ta sanar da sanar da sakamakon zaben ranar 27 ga wata oktoba 2024, na wannan shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *