Mene ne Gaskiyar Korar Seaman Abbas Daga Rundunar Sojin Nigeria Bayan An Sako Shi?

Spread the love

An saki sojan ruwan Najeriya da ake daure da shi na tsawon shekaru shida, mai suna Seaman Abbas Haruna, wanda matarsa ta kai koke a shirin Barekete Family na kafar yaɗa labarai na Human Rights.

A safiyar Juma’a Saeman Abbas da matarsa Hussaina sun bayyana a cikin shirin na Brekete Family, inda matarsa ta sanar cewa sojoji “sun kori shi daga aiki.”

An hango Seaman Abbas tare da matarsa a cikin dakin gudanar da shirye-shirye na Human Rights Radio (Berekete Family) a safiyar yau.

Sai dai har kawo wannan lokacin, Rundunar Sojin Najeriya ba ta fitar da sanarwa a kan korar jami’in ba, kamar yadda ta saba.

Tun bayan bullar wannan batu kan tsare Abbas, sakamakon Zargi da ake Yi na Samun sabani da kwamandan sa, har ya shafe shekaru Shida a daure , ake Zargin ya samu tabin hankali kamar yadda matarsa ta bayyana.

Al’ummar Nigeria da kasashen ketare sun Yi Allah Wadai da mummunan matakin da aka Dauka kan Seaman Abbas, ba tare da bin ka’ida da Yancin Dan Adam ba kamar yadda dokar Nigeria da bayar cikin kudin tsarin mulkin ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *