Miji Ya Kashe Matarsa Saboda Taliyar Yara

Spread the love

Wani magidanci ya hallaka matarsa saboda taliyar yara a yankin Olota da ke Karamar Hukumar Alimosho a Jihar Legas.

Ana zargin magidancin ya yi wannan aika-aika ne bayan da ya dawo daga aiki ya samu matarsa ta dafa taliyar yara maimakon abincin da ya fi so.

Wata majiya da ta bukaci a saka sunanta saboda tsaro, ta ce mijin ya bar matar kwance bayan ya doke da dutse a kanta.

Majiyar ta ce wani makwabcin magidancin ne ya kira magidancin ya sanar da shi matarsa na cikin wani yanayi.

Makabtan ne suka garzaya da matar zuwa asibiti inda a can ne aka tabbatar da rasuwarta.

Yansanda sun kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja

Kotu ta aike da yar Tiktok Ramlat Princess gidan gyaran hali bisa zargin yada badala

Shaidu sun ce ’yan sanda sun cafke miji inda suna gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru a tsakaninsa da matarsa.

Amma rundunar ’yan sandan jihar Legos ta ce kawo yanzu ba a tabbatar da cewar mijin ne ya kashe matar ba.

Kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin ya ce suna kan bincike kuma da zarar sun kammala za su bayyana wa jama’a sakamakon binciken da suka samu.

Aminiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *