Ministan makamashi a ƙasar Saliyo, Alhadji Kanja Sesay ya yi murabus sakamakon yawaitar ɗaukewar wutar lantarki da ake fuskanta a kasar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar da Fadar Shugaban Kasar da ke birnin Freetown ta aika wa Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa AFP.
Tun bayan ajiye aikin, ministan Alhadji Kanja Sesay, ya ƙi cewa uffan dangane da murabus ɗin da ya yi tare da kin amincewa da bukatar tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai Faransa na AFP.
Tsohon ministan na makamashin kasar ta Saliyo na aiki ne ƙarƙashin kulawar shugaban kasar, Julius Maada Bio tare da wasu mutanen biyu.
- Kamata ya yi a riƙa yiwa malaman jami’a a Najeriya gwajin shan kwaya’
- Jirgin Air Peace ya yi saukar gaggawa a Legas
Murabus ɗin ministan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Saliyo ta rattaba hannu kan kwangilar Dalar Amurka miliyan 18.5 da wasu kamfanonin kasar Turkiyya guda biyu domin samar da hasken wutar lantarki a fadin kasar.