Ministan Tsaro, Matawalle, Ya Musanta Zargin tallafa Wa Yan Bindiga Da Kayan Abinci.

Spread the love

Karamin tsaron Nijeriya Bello Muhammed Matawalle, ya musanta zargin bayar da buhunan shinkafa 50, ga dan bindigar da ake nema ruwa a jallo a jahar Zamfara.

Matawalle ya bayyana hakan ne a wani martani da ya maryar, bisa zargin da wata kafar yada labaran Internet ta wallafa a shafin ta.
Ministan ya ce an yi hakanne domin watsa tsaba kaji su ci gaba da bata masa suna, musamman daga bangaren yan adawa.

Tunda farko dai shafin jaridar themailnewsonline.com, ne wallafa labarin, a ranar 28 ga watan Maris 2024, da cewar an fara rabon buhunan shinfar, da banagaren Ado Aliero, a ranar 17 ga watan Maris 2024.

Jaridar ta kara da cewa an ajiye buhunan shinkafar a gidan wani mai suna Audu Headmaster, mazaunin garin Yankuzo a karamar hukumar Tsafe kafin daga bisa a ba wa Ado Aliero dan bindigar dake cikin jerin sunayen da hukumomin tsaro ke nema ruwa a jallo.

A ranar 16 ga watan Yuli 2022, an taba nada Ado Aliero sarautar sarkin Yandoton Daji a jahar Zamfara.

Abaya dai rahotanni sun bayyana cewa, an bayar da tallafin buhunan shinkafar ta hannun wani mai suna Honorabul Musa Bawa Yankuzo, tsohon dan majalissar dokokin jahar Zamfara.

Sai dai Bawa Yankuzo , ya musanta zargin , da cewa lokacin da ake yada labarin yana kasar Saudiya domin yin Umara, lamarin da ya kara sanya, shakku kan sahihnacin labarin da aka wallafa na rabon kayan abincin ga dan bindigar.

Itama kafar yada labaran Zamfara Newsletter, wadda ta sake wallafa labarin, bayan ta jaridar themailnewsonline.com, ta wallafa shi, inda ta tabbatar da cewa labarin kanzon kurege ne, da bashi da tushe balle makama , kawai ana son yin amfani da wata dama ce don bata sunan tsohon gwamnan jahar kuma ministan tsaron Nigeria.

jaridar ta Zamfara Newsletter, ta ce maitaimaka wa gwamanan jahar Zamfara Dauda Lawan Dare, kan harkokin yada labarai, Abdul Balarabe, ne ya tabbatar mu su da labarin rabon shinkafar.

Haka zalika wata kungiyar matasa ta Arewa Youth for Peace, ta soki gwamnan jahar Zamfara Dauda lawan, da rashin tabuka wani abun azo agani a kan harkar tsaro dubu da tarin matsalolin da jahar ke fama da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *