Miyetti Allah ta nemi hukumomin Najeriya su saki shugabanta Bello Bodejo

Spread the love

Ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta nemi gwamnatin Najeriya ta gaggauta sakin shugabanta Bello Abdullahi Bodejo wanda ta ce sojoji sun tsare.

Kakakin ƙungiyar na ƙasa, Muhammad Tasiu Sulaiman, ya faɗ wa BBC cewa suna cikin tashin hankali saboda rashin sanin halin da shugabansu yake ciki.

Zuwa yanzu rundunar sojin Najeriya ba ta ce komai ba game da kama shugaban ƙungiyar makiyayan.

“Maigidanmu Bello Boɗejo yana dawowa ne sai ya tarar da wata matsala tsakanin wani soja da wasu yaran makiyaya. Sojan ya harbi shanu, su kuma yaran sun yi masa duka har suka jikkata shi sosai,” in ji shi.

“Washegari sojoji daga bataliyar 177 suka aiko suna nemansa, sai suka tsare shi. Mun jira amma bai dawo, kuma ba mu san me ya faru ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *