Rundunar dakarun ƙasashen da ke yaƙi da ƴan bindiga MNJTF ta sanar da kashe ƴan ƙungiyar Boko Haram biyu tare da ƙwace alburusai a garin Mora na ƙasar Kamaru.
Bayanin na ƙunshe cikin wata sanarwa jami’in yaɗa labaran rundunar, Lieutenant Kanar, Abubakar Abdullahi ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta ce a ranar 10 da 19 ga watan Fabarairu kuma, wasu ƴan Boko Haram sun miƙa wuya ga sojoji da ke Litri a Chadi da Doron Baga a Najeriya. An kuma gano makamai da alburusai a hannun ƴan ƙungiyar da suka tuba.
MNJTF ta ƙara da cewa ƙoƙarin dakarunta ya sa an dirar wa wasu ƴan ta’addan da ke Bagasola a Chadi tare da ƙwato kwale-kwale uku cikin wasu kayan da aka gani a hannun mutanen.
A wani samame na daban kuma a ranar 19 ga watan Fabarairu, sojoji sun gano wasu fanko da ake amfani da su wajen haɗa abubuwan da ke fashewar, an kuma dakusar da ƙarfin da ƴan bindigar ke da shi a yankin.
A ranar Talata kuma, sojojin saman Chadi sun kai hari kan mafakar ƴan Boko Haram da ke kusurwar tafkin Chadi ta kudanci kusa da iyakar Chadi da Kamaru da Najeriya, lamarin da ya kai ga kashe ƴan ta’adda da dama tare da lalata makamansu. An kuma ga ƴan bindiga da dama na faɗawa tafkin daga kwale-kwalensu kuma ana tunanin sun mutu.
A jamhuriyar Nijar kuma, sojoji sun tarwatsa wani yunƙuri na safarar makamai a arewacin Nguigmi kusa da iyakar Nijar da Chadi.
Samamen da sojojin suka kai kan lokaci ya sa an kama tarin makamai – bindigar AK47 guda shida da ƙunshin alburusai da kwanson zuba alburusan.
Sanarwar ta ƙara da cewa duk da waɗannan nasarori, sojoji biyu – ɗaya daga Najeriya, ɗayan kuma daga Chadi sun rasa ransu yayin da uku kuma suka samu raunuka.
Rundunar ta MNJTF ta yi wa sojojin da suka rasa ransu addu’a inda ta ce ta duƙufa wajen samar da zaman lafiya da tsaro tare da inganta abubuwan da suka kamata wajen bunƙasa tattalin arziki da shige da ficen mutane ba tare da shinge ba a tafkin Chadi.