Mota ta take matashin da ya zare Danbuda ya kwace wayar wata mata a Kano

Spread the love

Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da samun rahoton wani matashi da ya zare Dan bida ya kwaci wayar wata mata a yankin Unguwar gidan Zoo a jihar, lamarin da ya kai ga mota ta take shi lokacin da yake tsallaka titi.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano ,SP Abdulahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

TALLA

Kiyawa ya ce ya samu rahoton faruwar al’amarin inda aka nemi daukinsu domin su kai matashin Asibiti.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana halin da matashin ya ke ciki ba .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *