Muguwar Kaddara Ta Sa Na Shiga Kannywood —Hafsat

Spread the love

Jarumar Kannywood Hafsat Hassan, wadda aka fi sani da Ammi, ta bayyana shigarta masanana’anar a matsayin muguwar kaddara.

Ammi wadda ta taka rawa a fina-finai irinsu Alaka, Ke Duniya, Surukan Zamani, Uwar Gulma da sauransu, ta ce ta yi da na sanin shiga Kannywood.

“Gaskiya na yi da-na-sanin shigata fim,” in ji jarumar, tana mai cewa sai da ta shiga Kannywood ta gane cewa ashe kallon kitsen rogo take wa masana’antar.

Ta bayyana cewa a rayuwarta ba ta taba ganin rashin tarbiyya ba kamar abin da gane wa kanta  da ta shiga masana’ntar.

“Da muka je [location], sai in ga a daki daya za a sa maza biyu mata biyu a kan gado ana kwance.

Yan sanda sun gurfanar da matashin da ake zargi da Dabawa abokinsa Kwalaba.

“To a lokacin ban taba fita wani gari aiki ba, sai nake mamaki to wce irin rayuwa na kawo kaina?”

Jarumar ta ce, “A Kannywood ne wannan kujerar nan (ta mutum daya) za ku iya zama mutum uku, mata da maza.”

A cewarta, “Na taso a gidanmu da ’yan uwana maza, amma ban taba ganin na yi kusanci da maza bai sai a Kannywood,” in ji ta a hirarta da Freedom Radio.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *