Amadadin daukacin Al’ummar Kananan Hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure baki daya muna kira ga Al’umma a wadannan kananan hukumomin guda 3 dama Jihar Kano baki daya, da su yi watsi da duk wata sanarwa ko wasu maganganu na batanci da za su ji ana yi Kan Maigirma Wakilin Kananan Hukumomin RAKIBU a Majalisar Kasa *RT Hon Kabiru Alhassan Rurum.*
Mun Sami labarin yadda shugabancin karamar hukumar Rano da na Bunkure da wasu cikin Dattawa marasa kishin Kananan hukumomin ke kokarin sai sun barranta kansu da Jama’ar kananan hukumomin da wakilinsu abin son su Wanda yake hidimta wa yankin Koda yaushe.
Muna kira ga Jama’ar wannan yanki dama na Jihar kano kada ku damu dajin duk wasu kalamai da za’ai akan TURAKIN RANO domin wadanda zakuji sunyi a RADIO ko ta SOCIAL MEDIA biyan su kudi aka yi, don su yi hakan ba don son ransu ba Kuma ba wai dan Abinda za su fada gaskiya ne ba..
Ko karamin Yaro bama a kananan hukumomin RAKIBU ba, a Jihar kano ma yasan *RT Hon Kabiru Alhassan Rurum* na kokari Sosai wajen yiwa Al’ummar sa Ayyukan raya kasa da Kuma kawo musu abubuwan Ci gabansu, kada wani Abu da zaka fada da zaisa Jama’a su yarda da kai a kokarinka na suka ko bata RURUM a idon Mutanen garinsu ko a Rano ko a Kibiya bare Kuma a Bunkure..
Mai makon haka Muna kira ga shugabannin wadannan kananan hukumomin Rano NAZIRU YA’U dana Bunkure AB MAHMUD da ku maida hankali wajen yin abinda zaku iya yiwa Jama’ar yankin ku kafin ‘Yar damar da aka Ara muku ta kubuce domin da ku da wadanda suke sa ku kuyi fada ko ku muzanta TURAKI bazaku iya rabin rabin Abinda yakewa Jama’ar RAKIBU ba…
Muna Kuma fatan Jama’a karku biye musu akan duk wata fitina da zasu bijiro da ita a watannan kananan hukumomin,, ku sani shi TURAKIN RANO yayi muku nisa ta ko ina Kuma baida lokacin rigima yanxu aikin yadda zai sauke nauyin Alumma ne a gabansa domin Jama’ar sa na tare dashi kamar yadda suke fada a tarukan da Yayi da su cikin makonni biyun da suka gabata..
Muna kira ga Hukumomin tsaro dasu sanya idanu akan duk wadanda zasuyi kokarin tada hankalin Al’ummar mu tare da daukar matakin daya dace..
Mungode muku JAMA’AR RAKIBU..
*Fatihu Yusuf Bichi*
*Media Aide to Rurum.*
*Nov 15th, 2024.*