Wani mummunan Hatsarin Mota ya Yi sanadiyar rasa rayukan mutane 2 , ya yin da Direban motar ya jikkata tare da rasa hannunsa guda Daya, sai kuma Jakuna guda 40 wadanda suka mutu a sanadiyar Hatsarin.
Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Jigawa DSP Shisu Lawan Adamu, ne ya tabbatar da hakan ga Jaridar idongari.ng , a ranar Litinin 4 ga watan Nuwamban 2024.
DSP Shisu Lawan, ya ce lamarin ya Faru ne , a Shuwarin karamar hukumar Kiyawa ta jahar, a lokacin da direban motar Mai suna Mohd Hassan Dan Shekaru 34, mazaunin karamar hukumar Potoskun ta jahar Yobe, ya yi Lodin Jakunan daga Yobe da niyyar Kai su jahar Enugu.
A kalla dai Jakuna 100 ne a cikin motar da Fasinjoji guda 2 a Saman motar, Inda akan hanyar ce direban ya kasa sarrafa motar har ta fadi, a Garin Shuwarin dake jahar Jigawa.
- ‘Yaranmu na cikin ƙunci bayan kama su da gwamnatin Sokoto ta yi kan zanga-zanga’
- dumi-dumi,Tinubu ya ba da umarnin sakin yaran da aka gurfanar a kotu kan zanga-zanga
Fasinjojin biyu da suka rasu sun hada da , Innani Abubakar Mai shekaru 45 da kuma Kalifa Adamu Mai shekaru 30 dukkan su mazauna Potoskun.
Rundunar Yan Sandan jahar Jigawa ta ce Tuni, aka garzaya da direban motar zuwa asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH) don bashi kulawar gaggawa.