Gamayya kungiyoyi matasan Arewancin Nigeria, ta tsakiya ta dakatar da fafutikar da ta ke yi, ta neman tsige Dr.Abdullahi Umar Ganduje daga matsayinsa na shugabancin jam’iyyar APC.
Shugaban gamayyar kungiyoyin, Hon Abdullahi Sale Zazzaga , ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da manema labarai a ranar laraba.
Zazzaga ya ce manyansu ne su ka ja hankalinsu dan su dakatar wannan fafitika musamman duba da cewar taron kwamatin zartarwa na jam’iyyar na karatowa.
Zazzaga ya ce, “komai da kaga ana yi , ana yi ne bisa dalili Muna siyasa dan neman yanci ne kuma bisa doron dalili.
Dalilin kuma shi ne domin cigaban yankinmu da al’umarmu da zaman lafiyar su da kuma bunkasar tattalin arzikinsu.
“Abinda ya faru shi ne, mun yi fafutika,kowa da yake fadin kasarnan ya san mun yi fafitika,kuma ba daina fafitika za mu yi ba.
“Muna wannna fafitika ne saboda ci gaban al’umma,amma sai dai komai da mu ke yi muna da manya. A cikin wannan tafiya da mu ke yi manyanmu sun kiramu sun zauna damu, kuma sun ce lokaci ya yi da za mu tsaya da wannnan fafutika saboda duk wanda ya kamata ya jimu ya jimu, wanda yakamata ya yi magana ya yi magana, sun umarce mu da dakatar da wannan fafitika tun da taron kwamatin zartarwar na jam’iyyar na karatowa nan da kwanaki.
“Sun ce mu jira muga me kwamatin zai yi akai, duk abin da NEC ta yanke daga nan sai mu san mu san matakin da za mu dauka na gaba.”
- Kawu Sumaila Ya Cancanci Rike Kowanne Irin Kwamiti : Rurum
- Kotu Ta Dage Ci Gaba Da Sauraren Shaidu A Shari’ar Da Ake Zargin Matashin Da Ya Cinnawa Masallata Wuta A Kano.