Mun dauki kaddara game da masarautar mu da aka rushe’

Spread the love

Sarkin masarautar Gaya daya daga cikin masarautu biyar da gwamnatin jihar Kano ta rushe, ya ce sun karbi wannan al’amari hannu-bibiyu a matsayin wata kaddara.

Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir ya shaidawa BBC cewa haka Allah ya nufa, don haka ba sa jin haushin kowa:

”Ai kowa wannan abu ya same shi, ba zai ji dadi ba ,to amma Allah ne ya kawo ka, komai akwai ajalinsa. Allah ya rubuta dama tun kafin a haifemu hakan za ta kasance, saboda haka mu ba mu jin haushin komi.Wannan yin Allah ne mun karbe shi hannu-bibiyu” in ji shi.

Mai martaba Sarkin Gaya ya yi bayani kan halin da ake ciki bayan umurnin awa 48 da gwamnan jihar Kano ya bayar ga sarakunan da su fice daga masarautunsu.

A cewarsa ‘su ma su bin doka ne, kuma ba su ma bari awanni sun cika, suka bi doka suka fita’

An dai samu wasu a masarautar Kano da suka garzaya kotu har ma suka samo oda ta kotu da ta dakatar da wannan tsari gaba daya .

Sai dai mai martaba sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir ya ce sam ba su yi wannan tunani ba:

‘’Mu masu karbar kaddara ne,haka Allah ya so kuma haka za a yi dole, ba mu da niyyar mu je wajan shariah,mun karbi kaddara , mun godewa Allah’’

Sarkin ya ce fatansa ga masarautar Gaya da alummar Kano shi ne Allah ya ba su zaman lafiya da arziki mai dorewa kuma ya zaunar da su lafiya.

Ya kuma yi kira ga alummar masarautar Gaya da su yi hakuri

Bayannai sun ce majalisar dokokin jihar Kano za ta zauna ta yi nazari akan dubu yiwar ko bukatar samar da sarakuna masu daraja ta biyu.

Game da haka ne sarki ya ce a guje zai karbi duk wani tayin sarki mai daraja ta biyu duk da cewa shi sarki ne mai daraja ta daya kafin aka soke

‘’Za mu karba a guje ma kuwa, tunda mun gajeta’’

”Mu a wajan mu jama’a ce a gaban mu,duk abinda aka ce mu zo mu yi don jama’ar mu, mu taimaka mu su, za mu yi shi saboda haka mu ba mu da haushin kowa mun karbi wannan kaddara, haka Allah ya so” in ji shi .

A makon nan ne Majalisar dokokin jihar Kano ta yi gyara kan dokar masarautun jihar, abin da ya sa aka rushe masarautu biyar ciki har da masarautar ta Gaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *