Mun gaji bashin sama da naira biliyan 200 a jihar Rivers – Fubara

Spread the love

Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gaji wasu ayyuka 34 da ba a kammala ba waɗanda kuɗinsu ya kai sama da naira biliyan 225.279, waɗanda suka bazu a ƙananan hukumomi 13 na jihar.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa, a karkashin jagorancinsa, gwamnatin jihar Ribas ta bayar da wasu sabbin ayyukan titina guda tara wadanda kudinsu ya kai naira biliyan 534.332.

Ya bayyana rikicin siyasar da ya ɓarke tsakaninsa da ministan Abuja, Nyesome Wike cikin watanni uku da hawarsa kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023, a matsayin wani mummunan alamari.

Sai dai gwamnan ya tabbatar da cewa yanayi mafi muni ya wuce, domin gwamnatinsa ta samu nasarar kare hakkinta na gudanar da mulkin jihar tare da tabbatar da ci gabanta cikin ‘yanci da walwala, ba tare da wata tangarda ba.

Gwamna Fubara ya bayyana haka ne a lokacin da yake ƙaddamar da wani asusun gudanar da aiki da katin shaida domin bikin cika shekara guda da hawa kan mulki, wanda aka gudanar birnin Fatakwal.

Gwamna Fubara ya yi nuni da cewa, tun bayan rikicin, abubuwa da dama sun canja a fagen siyasa, kuma ya ci gaba da tsayawa tsayin daka kan alkawarin da ya ɗauka shekara guda da ta wuce na bai wa jihar Ribas fifiko, da kare muradunta, da tabbatar da cewa al’ummar jihar sun samu rabon dimokuradiyya da shugabanci na gari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *