Mun gano matsalar da ta kawo rashin wuta a rewacin Najeriya – TCN

Spread the love

Kamfanin samar da lantarki na Najeriya TCN ya ce ya gano abin da ya haifar da matsalar rashin wutar lantarki a wasu yankunan arewacin ƙasar.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, kamfanin ya ce layin samar da lantarki na Ugwuaji-Apir 330-kilovolt ne ya samu matsala.

A ‘yan kwanakin baya-bayan ne wasu yankunan arewacin ƙasar suka fuskanci matsalar katsewar wutar lantarki, lamarin da TCN ya alaƙanta da faɗuwar layin Ugwaji–Apir.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun daraktan hulɗa da jama’a na kamfanin, Ndidi Mbah, ya ce an gano matsalar ne a yankin Igumale na jihar Benue.

Mista Mbah ya ce sai a ranar Laraba ne kamfanin ya gano haƙiƙanin abin da ya faru.

Ya ƙara da cewa tuni kamfanin ya kammala shirye-shiryen tattara kayan aikin da yake buƙata domin fara gyaran layin a wurin da abin ya faru a yau Alhamis.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *