Mun gano wata ƙungiyar addini da ke samar wa ‘yan ta’adda kuɗi – EFCC

Spread the love

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC ta ce ta gano hannun wata ƙungiyar addini da ke taimaka wa ‘yan ta’adda wajen samun kuɗaɗen gudanar da ayyukansu na tayar da hankalin ƙasar.

Shugaban hukumar Ola Olukoyede ya yi wannan bayanin yayin wata tattaunawa ta kwana ɗaya da aka shirya a Abuja a yau Laraba.

Yayin jawabi a taron mai taken: “Matasa da Addini da kuma Yaƙi da cin hanci da rashawa”, Olukoyede ya ce an samu wata ƙungiyar addini da laifin kare wasu kuɗaɗe da ake zargi na sata ne bayan da aka samu kuɗaɗen a asusun bankin ƙungiyar.

“An samu wata ƙungiyar addini a ƙasar nan da ke boye wa ƴan ta’adda kuɗaɗe. Mun yi binciken da ya kai mu ga samun wasu kuɗaɗen sata a hannun wata ƙungiya ta addini.”

Majalisar Wakilan Najeriya ta sanya wa’adin kammala gyaran tsarin mulkin kasar

“Lokacin da muka tunkari ƙungiyar kan batun yayin aiwatar da bincikenmu, sai aka ba mu umarnin hana ci gaba da aiwatar da binciken namu,” a cewar shugaban na EFCC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *