Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta tabbatar da kama malan Audu, a yankin unguwar Dorayi bisa Zargin sa da Jagorantar harkar daba da kuma siyar da yaransa kayan maye.
Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadi 10 ga watan Nuwamban 2024.
Kiyawa ya ce Wanda Ake Zargin shi ne Mai gidan ” Gundura” Wanda aka kama a kwanakin baya a yankin unguwar Dorayi , bisa Zargin sa aikata daba.
Binciken Yan Sanda na farko-farko ya tabbatar da cewa Malan Audu, shi ne Wanda yake siyar da kayan maye, a matattarar Yan dabar Kafin asha a Yi mankas sannan a farwa al’umma.
Rundunar Yan Sandan ta kara da cewa, yanzu haka an samu saukin aiyukan daba da kwacen waya sakamakon daukar matakai da kuma gudunmawar da al’umma suke bayar wa a Koda yaushe.
A karshe Rundunar ta ce Malan Audu da kuma Gundura suna Hannun Yan Sanda a tsare bisa umarnin kotu don fadada bincike akan su kuma da zarar an kammala za a Gurfanar da su a gaban kotu.