Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce jami’an tsaro sun kama wasu mutane da ake zargi da bai wa masu garkuwa da mutane bayanan sirri a birnin Abuja.
Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin wani babban taro da ya yi da shugabannin ƙananan hukumomi da sarakunan gargajiya da jami’an tsaro da mazauna yankin Gwagwalada a birnin.
Duk da cewa ministan bai bayyana adadin mutanen da aka kaman ba, ya buƙaci mazauna yankin Gwagwalada su kwantar da hankalinsu, saboda a cewar za a samu ci gaba a yanayin tsaron birnin cikin kwanaki masu zuwa.
Mista Wike ya kuma umarci kwamishinan ‘yan sandan birnin ya gaggauta samar da ƙarin ofisoshin ‘yan sanda har guda biyu a ƙaramar hukumar Gwagwaladan.
Birnin Abuja dai a baya-bayan nan na ci gaba da fuskantar matsalar tsaro musamman a makonnin baya-bayan nan inda masu garkuwa da mutane ke ci gaba da sace mutane domin neman kuɗin fansa.