Mun kama mutumin da ya kitsa harin jirgin ƙasa na Kaduna – ‘Yansandan Najeriya

Spread the love

Rundunar ‘yansandan Najeriya ta ce ta kama mutumin da ya kitsa hari kan jirgin Abuja zuwa Kaduna, inda aka yi garkuwa da mutane da dama a watan Maris na 2022.

A cewar rundunar, an kama Ibrahim Abdullahi wanda aka fi sani da Mande bayan tattara bayanan sirri a yankin ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Haka nan, mai magana da yawun rundunar ‘yans sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi, Mande da sauran tawagarsa ne suka sace ɗaliban Jami’ar Greenfield.

“A ranar 12 ga watan Janairun 2024, dakarun yaƙi da garkuwa da mutane na Kaduna suka yi wuf tare da kama Mande a kusa da gadar sama ta Rido da ke kan titin Abuja zuwa Kaduna,” a ACP Olumuyiwa Adejobi.

A ranar Alhamis ne rundunar ta gabatar da Mande tare da wasu mutum 30, waɗanda ta ce “sun sha addabar” mazauna yankunan da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja ta hanyar sacewa da kuma kashe matafiya.

“Ana kallon Mande a matsayin jagoran ‘yanfashi kamar Bello Turji, da Dogo Gide,” in ji kakakin ‘yansandan.

Wannan ne karon farko da jami’an tsaro suka ce sun kama wani da zargin hannu a kai hari kan jirgin ƙasan, wanda gwamnatin Najeriya ta zargi ƙungiyar Boko Haram da kaiwa.

Majiyoyi daga asibitin 44 na jihar Kaduna da aka kai wasu daga cikin mutanen da harin da ‘yan bindigar suka kai kan jirgin da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna sun ce mutum bakwai ne suka mutu.

Kazalika sun ce mutum ashirin da biyu suka jikkata, cikinsu har da tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Wakkala.

A cikin watan Maris ɗin 2022 ne, wasu mahara ɗauke da muggan makamai suka kai hari kan jirgin ƙasan fasinja da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, ɗauke da ɗaruruwan fasinjoji a kusa da garin Katari a cikin jihar Kaduna.

A yayin harin, ‘yan bindigar sun fasa nakiyoyi tare da buɗe wuta kan fasinjoji, abin da ya yi sanadin mutuwar wasu, wasu da dama kuma suka ji raunuka, sannan ‘yan fashin suka sace fiye da mutum 60.

Daga bisani dai, an riƙa sako fasinjojin rukuni-rukuni, inda aka saki rukunin ƙarshe da ya ƙunshin mutum 23 a farkon watan Oktoban 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *