Mun kama sojan da ya harbe saurayi yayin zanga-zanga a Zariya — Sojoji

Spread the love

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kama sojan da ya kashe wani matashi yayin zanga-zangar yunwa a Zariya, Jihar Kaduna.

Aminiya ta ruwaito yadda wani soja ya harbe wani matashi mai suna Isma’il Muhammad a yankin Samaru da misalin ƙarfe 9 na safiyar ranar Talata.

Lamarin ya faru ne a titin Sarkin Pawa, inda Muhammad da iyayensa suke zama.

Mahaifiyar mamacin, Zainab Sani, ta ce yana wasa tare da abokansa da ɗan uwansa a ƙofar gidansu.

Ta ce lokacin da suka ga sojojin na zuwa, sai suka gudu tare da rufe ƙofa, amma sojan ya bi su ya harbi kofar ya kashe saurayin.

Babban Kwamandan Runduna ta 1, Manjo-Janar M.L.D. Saraso, ya ziyarci iyalan mamacin domin yi musu ta’aziyya.

Ya tabbatar musu cewar za su gudanar da cikakken bincike kan lamarin sannan ya nemi duk wanda yake da wata shaida kan lamarin ya miƙa wa hukumomin tsaro.

Saraso ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici kuma ya shawarci al’umma su zauna lafiya tare da kasancewa masu bin doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *