Mun kashe ƴan ta’adda dubu takwas a Najeriya cikin 2024 – Sojoji

Spread the love

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe ƴan ta’dda 8,034 daga farko zuwa ƙarshen shekara ta 2024.

Wata sanarwa da darektan yaɗa labarai na rundunar, Manjo-janar Edward Buba ya fitar, ta ce an samu nasarar ne a samame daban-daban da sojoji suka kai yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma da arewa maso tsakiya da kuma sauran yankunan ƙasar.

Ya ce an kama wasu ‘ƴan ta’dda’ 11,263 da kuma ceto mutum 6,376 da aka yi garkuwa da su.

“Mun kuma samu nasarar ƙwato makamai 8,216 da harsasai 211,459. Mun kuma daƙile yunkurin satar ɗanyen mai da kuɗinsa ya kai sama da naira biliyan 57,” in ji Buba.

Sai dai duk da irin waɗannan nasarori da rundunar sojin ke ayyanawa, Najeriya na ci gaba da fama da matsalar tsaro a yankuna daban-daban na ƙasar.

Ko a cikin kwanakin nan an samu ɓullar wata sabuwar ƙungiyar ƴan bidiga arewa maso yammacin Najeriyar, wadanda ake kira Lakurawa.

Haka nan ma a baya-bayan nan ƙungiyoyin ƴan bindiga sun riƙa dasa nakiyoyi a kan hanyoyin mota a jihar Zamfara, lamarin da ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *