Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa ta shirya tsaf don tabbatar da tsaro, a ziyarar aiki da uwar gidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, za ta kai jihar a ranar 12 ga watan Fabrairu 2024.
Kwamishinan ‘yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a Kano.
Gumel ya ce sun samar da isassun jami’an tsaro domin tabbatar da uwar gidan shugaban kasa ta kammala ziyarar da zata kawo kano lami lafiya .
Na kamu da cutar tsananin damuwa bayan rabuwa da matata :Zango
Yansanda sun kama mutanen da ake zargi da safarar ƙananan yara a Abuja
Gumel ya ce rundunar ta dauki kwararan matakan tsaro domin tabbatar da ziyarar lafiya.
“Mun tattara isassun jami’ai masu dauke da makamai domin bai wa uwar gidan shugaban kasa kariya kafin ziyarar, da lokacin da kuma bayan ziyarar,” in ji Gumel.
Kwamishinan ya kuma ce tuni rundunar ta fara shirin “Operation Show Force” tare da sauran hukumomin tsaro domin nuna shirin su kan ziyarar uwar gidan.
Ya bayyana cewa an dauki matakan ne domin bai wa mazauna jihar damar tarbar uwar gidan shugaban kasar da mukarrabanta ba tare da wata barazana ta tsaro ba .
Kwamishinan ya shawarci shugabannin jam’iyyun siyasar jihar da su ja hankalin magoya bayansu da su nisanci duk wani nau’in tashin hankali da yan daba, kafin ziyarar uwar gidan shugaban kasa da kuma bayan ziyarar.
Gumel ya ce: “Ba za mu amince da duk wani aiki da zai kawo rudani kafin ziyarar, lokacin da kuma bayan ziyarar ba.”
NAN