Mun Shirya Tunkarar Shekarar 2025 Da Sabbin Dabarun Aiki A Kano: Shehu Rabi’u

Spread the love

 

Rundunar yan sintiri ta bijilanti a jihar kano, ta bayyana yadda suka gudanar da aikace aikacen ta a shekarar 2024, da muke bankwana da ita tare da bayyana shirin da suka yi na tunkarar sabuwar shekarar 2025.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin Babban kwamandan bijilanti na kano Alhaji Shehu Rabiu,  yayin zantawar sa da manema labarai a birnin Kano.

Ya ce sun gudanar da manya manyan aikace aikacen da ba za su manta da su ba musamman a shekarar da muke kokarin bankwana da ita , domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar kano a sassan kananan hukumomin kano 44.

Aikace aikacen sun hadar da kama bata garin mutane masu haurawa gidajen jama’a dama su satar kayan Gona, masu kwacen wayoyin al’umma harma da masu garkuwa da mutane a wasu sassan kauyukan karkara.

 

Yana kara da cewar, daga cikin nasarorin da suka samu a shekarar 2024 sun hadar da gudanar da aikin zaben kananan hukumomin kano 44 da ya wakana, wajen tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma lokacin zanga zangar tsadar rayuwa, tsaron rayuka yayin rikicin masarautar kano, dunkulewar bijilanti ta zama daya a jihar kano da Ginin katafariyar Babbar shalkwatar rundunar yan bijilanti da gwamnatin kano ke yi a yanzu da dai sauran su.

Shehu Rabiu, ya Sha alwashin jami’an bijilanti a jihar kano, za su ci gaba da aikin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar ba dare ba rana domin tabbatar da inganta harkokin tsaro a fadin kano domin gudun kwararowar bata gari daga makotan jihohi.

Yana mai nuna damuwar sa dangane da rasa rayukan wasu daga cikin yan bijilanti ya yin da suke tsaka da aikin tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kara da cewar, tuni suka shirya tunkarar shekarar 2025 da wasu sabbin dabarun aiki na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar kano musamman a loko da sakon unguwannin kano.

Kwamandan ya bukaci al’umma masu hannu da shuni da  ‘yan kasuwa da daidaikun jama’a , da su kasance masu taimakawa yan bijilanti da kayan aiki da biyan kudin hayar ofisoshin su harma da bayanan sirri da zarar sunga motsin abinda ba su amince da shi ba domin kawo mu su daukin gaggawa.

Daga nan ya yaba wa gwamnatin kano kan yadda ta ke ba su gudummawa wajen inganta harkokin tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *