Rundunar Yan sandan jahar Kano, tare da sauran gamayyar hukumomin tsaron jahar sun Shirya tsaf, don bayar da cikakken tsaro a Bukukuwan karamar Sallah.
Kakakin rundunar Yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani faifen Murya da ya aike wa Jaridar Idongari.ng, a Ranar Talata .
Sanarwar ta ce Kwamishinan Yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya yi kira ga al’ummar da za suje sallar idi su kaucewa daukar duk wani Abu da zai haifar da zargi ko firgita jama’a.
Rundunar Yan sandan ta kuma gargadi iyaye su kula da yayan su, kasancewar a shekarun baya an samu rahotannin batan kananan yara.
- EFCC Ta Gano Naira Biliyan 30 A Wajen Betta Edu
- Al’umma Su Ci Gaba Da Aikata Aiyukan Alkairi: Dagacin Yankusa.
SP Abdullahi Kiyawa, ya Kara da cewa, a kiyayi bai wa kananan yara wadanda shekarun su bai Kai su tuka Ababen hawa ba, da kuma gujewa yin tukin ganganci ko gudun wuce sa’a da zai haifar hadura da kan jikkata al’umma koma rasa rai baki daya.
Kwamishinan Yan sandan jahar CP Muhammed Gumel, ya ce lokacin Bukukuwan Sallah lokaci ne na farin ciki ba na bacin ba, kuma lokacin ne da al’umma suke fita tare da ganawa da al’umma .
A karshe rundunar taja hankalin ma su kunnen kashi da suke Yunkurin fito wa don tayar da hankulan al’umma, ko yin kwacen waya, fadan daba da kuma fashi , rundunar ta ce, a shirye ta ke wajen murkushe batagarin, inda ta yi wa al’umma fatan alkairi a kuma kammala Bukukuwan Sallah lafiya.
- Kano: Yan Kasuwar Kaji Sun Koka Da Karancin Ciniki.
- Sojoji sun tarwatsa sansanin ƙasurgumin ɗan fashin daji a Zamfara